in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan hada kai da kasashen Afrika don sa kami ga ciniki da zuba jari cikin 'yanci
2018-04-18 11:14:36 cri

A jiya Talata, jakadan kasar Sin dake kasar Masar Song Aiguo ya halarci taron kara wa juna sani kan ci gaban da aka samu wajen kafa yankin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ta fuskar tattalin arziki, inda ya bayyana cewa, Sin na fatan kara hada kai da kasashen duniya, ciki har da Afrika don sa kaimi ga ciniki da zuba jari cikin 'yanci da sauki.

A wajen taron, jami'ai da masana daga kasashe daban-daban sun tattauna kan ci gaban da aka samu na kafa yankin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ta fuskar ciniki da kuma yankin raya masana'antu, wadannan kasashe sun hada da Sin, Masar, Nigeria, Habasha, Zambiya, Djibouti, Algeria, Mauritania da dai sauransu.

An ba da labari cewa, yawan kudin da aka samu daga cinikayya a tsakani Sin da Afrika ya kai dala bilyan 170, hakan ya sa Sin ta zama abokiyar ciniki mafi grima ga kasashen Afrika cikin shekaru 9 a jere, yawan kudin da Sin ta zuba ya kai dala biliyan 100, yawan kamfanonin Sin dake Afrika ya wuce 3100.

Ban da wannan kuma, ya zuwa yanzu, yankunan tattalin arziki da ciniki da Sin ta kafa a Afrika sun zarta 20, wadanda suka shigo da kamfanoni fiye da 360, yawan kudin da aka zuba ya kai kimanin dala biliyan 4.7, yawan darajar kayayyakin da aka samar ya kai dala biliyan 13, kuma yawan harajin da aka buga ya kai miliyan 560, ban da wannan kuma, yawan guraben aikin yi da aka samar ya kai dubu 26. Yankin hadin kai na ciniki tsakanin Sin da Masar na Suez, da yankin hadin kai na ciniki tsakanin Sin da Zambiya da kuma yankin hadin kai na ciniki Lekki tsakanin Sin da Nigeria sun fi taka rawa a fannin.(Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China