in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta ki amincewa da laifin da Habasha da Sudan suka dora mata dangane da gazawar tattaunawarsu kan madatsar ruwan da Habasha ke ginawa
2018-04-13 10:01:26 cri
Masar ta ki amincewa da laifin da Habasha da Sudan suka dora mata na gazawar tattaunawar kasashen uku, game da babbar madatsar ruwa da Habasha ke ginawa.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Masar ta fitar a jiya, ta mai da martani kan sanawar baya-bayan nan da ma'aikatun harkokin wajen kasashen Habasha da Sudan suka fitar, inda suka dora laifin gaza tattaunawar da suka shirya yi a farkon wannan wata a birnin Khartoum a kan Masar.

Sanarwar da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Masar Ahmed Abu Zeid ya fitar, ta ce Masar ta shiga tattaunawar 'bangarori 9' ta Khartoum da kyakkyawar manufa da kuma burin cimma yarjejeniyar aiwatar da umarnin kasashen 3.

An yi wa taron lakabi da 'bangarori 9' ne saboda ya kunshi ministocin harkokin waje da na albarkatun ruwa da shugabannin hukumomin leken asiri na kasashen 3.

Ahmed Abu Zeid ya yi bayanin cewa, Masar ta shiga tattaunawar ta Khartoum ne da nufin cimma mafita da za ta shawo kan rashin ci gaba da aka samu a tattaunawar kwararrun game da madatsar ruwan.

Ya kuma bayyana cewa, ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya aike da wasiku a ranar Laraba, ga takwarorinsa na Habasha da Sudan, ya na mai gayyatar su ga wani taro a birnin Alkahira domin ci gaba da tattaunawar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China