in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD ya yi kira samar da kafar watsa labarai mai 'yanci a Somaliya
2018-05-04 09:56:20 cri
Wakilin musamman na babban sakataren MDD dake kasar Somaliya Micheal Keating ya yi kira da a sakarwa kafofin watsa labarai mara, ta yadda za su rika gudanar da ayyukansu ba tare da wani tarnaki ba a kasar.

Jami'in wanda ya bayyana hakan albarkacin ranar 'yancin 'yan jaridu ta duniya da aka gudanar a jiya Alhamis, uku ga watan Mayu, ya kuma yaba da yadda 'yan jaridu a kasar ke gudanar da ayyukansu a daya daga cikin kasashe mafiya hadari ga aikin jarida a duniya.

A don haka ya bukaci masu tsara dokoki da su sake tattaunawa kan dokar kafofin watsa labaran kasar ta shekarar 2016 da aka yiwa gyaran fuska, su kuma ba da shawara kan sassan dokar dake bukatar gyara da kungiyar kafofin watsa labaran kasar ta gabatar a shekarar da ta gabata.

A cewar wani kwamitin kare hakkin 'yan jarida dake Amurka (CPI) har yanzu ba a hukunta kowa ba kan 'yan jaridu 26 da aka kashe cikin shekaru goma da suka gabata, kuma shekaru uku a jere ke nan ana ayyana kasar a matsayin ta baya ga dangi a duniya a fannin rashin bin kadun 'yan jaridun da aka kashe, kamar yadda sakamakon binciken kwamitin na CPI na shekarar 2017 ya nuna. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China