in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane kimanin dubu 500 na fama da ambaliyar ruwa a kasar Somaliya
2018-05-03 10:02:59 cri

Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed ya bayar da wata sanarwa a daren ranar 1 ga wata, inda ya bayyana cewa, mutane kimanin dubu 500 ne ke fama da ambaliyar ruwa a kasar a kwanakin nan, ciki har da mutane dubu 175 da suka rasa matsugunansu.

Shugaba Mohamed ya kara da cewa, gwamnatin kasar Somaliya na daukar matakai don tinkarar matsalar jin kai sakamakon abkuwar ambaliyar ruwan. Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su samar da taimako ga kasarsa. Ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta kafa kwamitin tinkarar matsalar domin taimakawa jama'a dake fama da bala'in. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China