in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ICRC ta bukaci a sako jami'ar ta da aka yi garkuwa da ita
2018-05-03 21:25:14 cri
Kwamitin kasa da kasa na kungiyar ba da agajin jin kai ta ICRC, ya yi kira da a sako wata jami'ar lafiya da aka yi garkuwa da ita a Mogadishu fadar mulkin kasar Somali.

Mataimakin shugaban ICRC a Somaliya Daniel O'Malley, ya bayyana cewa, wasu mutane dauke da makamai ne suka kutsa kai cikin harabar ofishin na ICRC da misalin karfe 8 na daren ranar Laraba, inda kuma nan take suka yi awon gaba da wata jami'ar jinya 'yar kasar Jamus.

Mahukuntan ICRC dai sun ce suna tuntubar sassa masu ruwa da tsaki daban daban, a wani mataki na kokarin ceto wannan jami'a. Sai dai sun ce ba za su yi karin haske, game da halin da ake ciki ba game da kokarin da suke yi na ceto ta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China