Fadar White House ta ce an shirya gudanar da taro tsakanin Shugaban Amurka, Donald Trump da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un, da misalin karfe 9 na safiyar ranar 12 ga watan nan, a Singapore.
Yayin wani taron manema labarai, kakakin fadar White House Sarah Sanders, ta ce tuni ayarin masu shirya ziyarar shugaban kasar suka isa Singapore, inda suke kokarin kammala duk wani shirye-shirye, kana za su kasance a can har sai an fara taron.
Da take bayanna cewa bangaren Amurka na shiryawa taron yadda ya kamata, ta ce ayarin Amurka dake iyakar da aka shata tsakanin kasashen Koriya 2, na ci gaba da tattaunawar diflomasiyya da ayarin Koriya ta arewa.
Ta kara da cewa, ana samun kyawawan sakamako da nasarori game da tattaunawar.
Bayan ganawarsa da Kim Yong Chol, wanda ya kai masa wasikar da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un ya aike masa, Shugaba Trump ya bayyana a ranar Jumma'ar da ta gabata cewa, zai gana da shugaban na Koriya ta arewa a ranar 12 ga watan nan a Singapore kamar yadda aka tsara tun farko. (Fa'iza Mustapha)