in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kim Jong-un ya gana da ministan harkokin wajen kasar Amurka
2018-05-10 10:49:33 cri

Kafar yada labarai ta kasar Koriya ta Arewa, ta ba da labari a yau 10 ga wata cewa, shugaban kasar Kim Jong-un ya gana da ministan harkokin waje na kasar Amurka Mike Pompeo, wanda ke ziyarar aiki a kasar. Yayin ganawar tasu, Kim Jong-un ya bayyana ganawar da za a yi tsakaninsa da takwaransa na Amurka, a matsayin ziyara mai muhimmanci a tarihi, kuma ya yi umurnin sakin wasu Amurkawa da Koriya ta Arewa ke tsare da su.

Rahoton ya ce, Kim Jong-un ya bayyana wa Mike Pompeo cewa, ganawar da za a yi za ta kasance matakin farko, wajen sa kaimi ga warware rikicin zirin, da bunkasa zirin yadda ya kamata a nan gaba.

Ban da wannan kuma, an ce, ziyarar Mike Pompeo a wannan karo, na isar da sako daga shugaban Amurka Donald Trump zuwa ga Kim Jong-un, don share fagen ganawa tsakaninsu.

Haka zalika, an bayyana cewa, Kim Jong-un da Mike Pompeo sun yi musanyar ra'ayi kan halin da ake ciki a zirin, da matsayin da shugabannin kasashen biyu suka dauka kan ganawar da za su yi, tare kuma da tattauna kan hakikanin matakin da za a dauka kan wannan ganawa. An ce, bangarorin biyu sun kai ga cimma matsaya daya bayan shawarwarin.

An ce, Donald Trump ya fidda sako ta yanar gizo cewa, Koriya ta Arewa ta riga ta saki Amurkawan su uku da take tsare da su. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China