Rahotanni daga Koriya ta Arewa DPRK na cewa, mahukuntan kasar na shirin dakatar da tattaunawa da bangaren Koriya ta Kudu ROK, saboda atisayin soja na hadin gwiwa da Koriya ta Kudun take yi da Amurka, matakin da Koriya ta Arewan ta bayyana a matsayin takala.
Bugu da kari, kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewan (KCNA) ya bukaci Amurka da ta sake tunani game da makomar ganawar da aka shirya yi tsakanin Amurkar da Koriya ta Arewa.
Sai dai kuma jim kadan bayan sanar da wannan rahoto, ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce tana ci gaba da kimtsawa ganawar da shugaba Donald Trump na Amurka zai yi da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un ranar 12 ga watan Yuni a kasar Singapore.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Heather Nauert ya bayyana cewa, har yanzu dai Amurka ba ta ji komai daga kasashen Koriyoyin biyu ba, da har zai sa ta canja ko dakatar da shirye-shiryen da take yi game da wannan ganawa.(Ibrahim)