in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya aike da wasika ga Kim, inda ya soke ganawar da suka shirya yi a Singapore
2018-05-25 09:32:03 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya aike da wasika ga shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, yana mai soke ganawar da aka shirya yi tsakaninsu, ranar 12 ga watan Yuni a kasar Singapore.

Cikin wasikar da fadar White House ta aike, shugaba Trump ya ce, duk da cewa ya sa ran zuwa Singapore don ganawa da shugaba Kim, bai dace a ce an yi ganawar a wannan lokaci ba, la'akari da fushi da kausasan kalamai dake kunshe cikin jawabin baya-bayan nan da shugaban Koriya ta Arewar ya yi.

Sai dai, Trump ya kara da cewa, yana sa ran ganawa da shugaba Kim wata rana.

A martaninta, Koriya ta Arewa, ta bayyana a yau Juma'a cewa, a shirye take ta tattauna da Amurka a ko wane lokaci.

A jiya Alhamis ne kuma, sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ya damu ainun da jin cewa shugaban Amurka Donald Trump, ya soke ganawar da ya shirya yi cikin watan gobe a Singapore, tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki game da batun, su ci gaba da tattaunawa don samun hanyar tabbatar da kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya cikin ruwan sanyi.

Shi ma shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu, cikin wata sanarwa da fadar Blue House ta fitar da sanyin safiyar yau Juma'a, ya bayyana takaicinsa game da soke ganawar, tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China