Lu ya bayyana haka ne a yayin manema labaru da aka shirya a yau Laraba a nan birnin Beijing, inda ya kara da cewa, yanzu an samu dama mai kyau wajen warware matsalar zirin Koriya a siyasanci, kuma kasar Sin na fatan bangarori daban daban, musamman ma Amurka da Koriya ta arewa za su yi amfani da wannan damar don warware sabanin dake tsakaninsu kan wannan batu. Baya ga haka, Lu ya ce, Sin za ta ci gaba da taka rawa kan wannan batun.
Rahotani na cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a jiya Talata cewa, mai yiwuwa ne za a samu jinkiri game da ganawar da za su tsakaninsa da takwaransa na kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un. (Bilkisu)