in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya ba da ra'ayi game da batun mayar da dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Burkina Faso
2018-05-27 16:40:55 cri
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso Alpha Barry a ranar 26 ga wata a nan birnin Beijing, tare da daddale hadaddiyar sanarwa ta kasashen Sin da Burkina Faso game da mayar da huldar diplomasiyya a tsakaninsu.

Wang Yi, ya bayyana a cikin sanarwar cewa, gwamnatin kasar Burkina Faso ta amince da Sin daya tak a duniya, gwamnatin kasar Sin gwamnati daya kawai ce dake wakiltar kasar Sin, yankin Taiwan muhimmin kashi ne na kasar Sin. Sin ta nuna yabo ga gwamnatin kasar Burkina Faso da ta dace da yanayin duniya na tsaida kuduri mai dacewa a fannin siyasa.

Wang Yi ya yi nuni da cewa, ka'idar Sin daya tak ka'ida ce da kasa da kasa suka amince da ita, wadda ke shafar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, kana shi ne tushen da Sin ta raya dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya. Bi da bi ne kasar Gambia, da Sao Tome da Principe, da Panama, da Dominica sun kulla ko mayar da dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar Sin, wanda ya kara yawan abokan huldar kasar Sin a duniya.

Wang Yi ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping yana maraba da shugaban kasar Burkina Faso Christian Kaboré da ya kawo ziyara a kasar Sin tare da halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a watan Satumba na bana, shugaba Kaboré ya nuna begensa na halartar taron kolin tare da yin shawarwari tare da shugaba Xi Jinping kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin da kuma Afirka da Sin..

A nasa bangare, Barry ya bayyana cewa, mayar da dangantakar diplomasiyya dake tsakanin kasarsa da kasar Sin ta dace da burin moriyar jama'ar kasarsa, kasar Burkina Faso ta amince da ka'idar Sin daya tak. Kasarsa ta Burkina Faso ta riga ta yanke dangantakar dake tsakaninta da yankin Taiwan, kuma ba za ta raya dangantaka ta gwamnati tare da yankin Taiwan ba. Kasar Burkina Faso tana fatan kafa dangantakar abokantaka a tsakaninta da kasar Sin, da yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin siyasa, tattalin arziki, zamantakewar al'umma, al'adu da sauransu, da samar da gudummawa wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China