Wang Yi ya bayyana cewa, kafuwar kungiyar G20 da bunkasuwarta, sun shaida ra'ayin bangarori daban daban, da ci gaban aikin kwaskwarima da kyautata tsarin duniya.
An shaida cewa, tsayawa kan ra'ayin bangarori daban daban, da kyautata tsarin duniya, da raya tsarin samun moriyar juna, sun dace da halin da ake ciki a duniya da kuma moriyar kasa da kasa. Kuma ya kamata a kafa sabuwar dangantaka tsakanin kasa da kasa, bisa burin yin hadin gwiwa da samun moriyar juna. Idan aka bi ra'ayin ba da kariya na kashin kai, hakan zai haifar da rufe kofa ga saura, da rufewa kai kofa. Don haka ya kamata kasa da kasa su yi kira ga yin hadin gwiwa da samun moriyar juna.
Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta zama kasa mai shimfida zaman lafiya da samar da gudummawa da tabbatar da odar duniya. Kaza lika Sin tana fatan yin kokari tare da kasa da kasa, wajen samar da kyakkyawar makoma a duniya. (Zainab)