in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Afrika ta kudu
2018-05-22 09:50:53 cri

Ministan harkokin waje na kasar Sin Mista Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Afrika ta kudu Lindiwe Sisulu a ran 21 ga wata bisa agogon wurin, yayin taron ministocin harkokin waje na G20 da aka kira a Buenos Aires na kasar Argentina.

A ganawar ta su, Mista Wang ya nuna cewa, Sin da Afrika ta kudu na ba da muhimmiyar gudunmawa, wajen gudanar da harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya cikin hadin kai, a matsayinsu na kasashe masu tasowa kuma masu girma a duniya. Ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na kawo alfanu sosai ga dukkanin duniya, kuma Sin na fatan kara hadin kai da Afrika ta kudu, wajen kiyaye dunkulewa da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, tare kuma da kyautata tsarin daidaito a duniya.

A nasa bangare kuwa, Mr. Sisulu ya ce, Afrika ta kudu na godiya sosai ga goyon baya da Sin take nuna mata, game da shirya taron shugabannin BRICS, yana kuma sa ran hadin kai da kasar Sin, don tabbatar da taro, da ziyarar da shugabannin Sin za su kai a Afrika ta kudu, tare kuma da samun ci gaba mai armashi tsakaninsu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China