in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi zai ziyarci Jamus da Belgium da Afirka ta kudu
2018-05-28 20:20:39 cri

Dan majalissar zartaswar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai ziyarci kasar Jamus, kana zai halarci taron masu ruwa da tsaki na manyan jami'ai, domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar Turai ta EU karo na 8, wanda zai gudana a birnin Brussels na kasar Belgium.

Kaza lika zai ziyarci Afirka ta kudu, domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar BRICS, taron da zai gudana tsakanin ranekun Laraba da Talatar mako mai zuwa.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Hua Chunying ce ta bayyana hakan a Litinin din nan. Ta ce Mr. Wang zai gudanar da wannan ziyara ne bisa gayyatar ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas, da babbar wakiliyar kungiyar EU mai lura da harkokin waje da tsara manufofin tsaro Federica Mogherini, da kuma ministar hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta kudu Lindiwe Sisulu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China