in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Ana fatan abokan hadin gwiwar Sin za su cika alkawarinsu
2018-06-02 16:21:55 cri
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kasarsa na fatan abokan hadin gwiwarta za su cika alkawurran da suka dauka.

Wang Yi, ya bayyana hakan ne jiya a birnin Brussels, yayin da yake zantawa da manema labaru tare da wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro Federica Mogherin.

Game da batun matsalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, Wang Yi ya ce, matsayin da Sin ta tsaya ya tabbatar da moriyarta, kana ya tabbatar da ka'idojin kasa da kasa da tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban. Ya ce kasar Sin ta zabi manufar girmama juna da samun moriyar juna cikin adalci, da kara tattaunawa da Amurka kan yadda za a gudanar da abubuwan da suka cimma daidaito kansu a baya, kuma ana fatan za a samu sakamako irin ma moriyar juna a karshe. Har ila yau, Wang Yi, ya ce Sin ta kan sauke nauyin dake wuyanta, kuma ta kan cika alkawurranta yayin da take raya dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, kuma tana fatan abokan hadin gwiwarta za su cika na su alkawurran. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China