Ministar wadda ta bayyana hakan yayin da take jawabi a bikin kafa tuta da aza furanni, don tunawa da ranar ma'aikatan wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa ta MDD da ya gudana a birnin Accrar kasar Ghana, ta ce a matsayinsa na mamba na rukunin hadiman babban sakataren MDD dake yaki da yin latata da cin zarafi yayin ayyukan wanzar da zaman lafiya, shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana ya bayyana karara cewa, zai taimakawa waje magance wannan mummunar ta'ada.
Don haka ta ce, gwamnati za ta dauki kwararan matakai kan duk wani mai kayan sarki ko farar hula da aka tabbatar ya aikata ba dai-dai ba yayin da yake gudanar da aikinsa na tabbatar da zaman lafiya, sabanin halayen kwarai da dakarun kasar ta Ghana dake ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD suka nuna a shekarun baya. (Ibrahim Yaya)