Gwamnan bankin Ernest Addison, ya alakanta matakin da bukatar daidaita rage hadarin faduwar darajar kudin kasar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma bukatar habaka ci gaban tattalin arziki.
A cewarsa, an rage hadarin faduwar darajar kudi da hauhauwar farashin kayayyakin a cikin lokacin da aka yi hasashe, yana mai cewa, yayin da ci gaban tattalin arzikin kasar da na duniya ba sa barazanar ga darajar kudi da hauhawar farashi a nan kusa, akwai bukatar sanya ido kan sauye-sauyen da aka samu a baya-bayan nan game da sharudan harkokin kudi da kuma tasirinsa kan rukunin kasuwar kadarori. (Fa'iza Mustapha)