in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana ta mayar da hankali kan yaki da cin hanci domin samun ci gabanta
2018-05-18 10:31:48 cri
Mataimakin Ministan harkokin wajen Ghana Charles Owiredu, ya ce Gwamnatin kasar ta mayar da hankali kan yaki da cin hanci domin inganta ci gabanta.

Da yake ganawa da manema labarai gabanin ranar bikin Tarayyar Afrika AU, Charles Owiredu, ya ce Gwamnati na shirya wani tsarin yaki da cin hanci na kasar, wanda ake sa ran zai tsara tare da nazarin abubuwan da ake bukata, wadanda za su taimaka wajen karewa da yaki da cin hanci ta hanyar yayata akidu na kwarai da kafa dokoki.

Ya kara da cewa, kirkiro ofishin mai shigar da kara na musammam, alama ce dake nuna kudurin Gwamnatin, na fatattakar cin hanci a dukkan matakai da kuma daidaita tafarkin makomar da kasar ta zaba.

A ranar Juma'a mai zuwa, wato 25 ga watan Mayu, ake cika shekaru 55 da kafuwar Tarayyar Afrika AU, a matsayin kungiyar hadin kan Afrika (OAU) a birnin Addis Ababa na Habasha a shekarar 1963.

Taken bikin na bana shi ne "nasarar yaki da cin hanci: hanya mai dorewa ta ci gaban Afrika"

Ministan ya yi kira ga dukkan al'ummar nahiyar, su kasance mutane na kwarai tare da bada tasu gudumnuwar da ake bukata na cimma daukacin burin tarayyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China