Saboda rage mummunan tasirin robobin, wani kamfanin kasar Ghana ya bullo da wata hanya ta sarrafa bolar robobin zuwa bulon kawata dabe na interlock da sauran kayakin gini.
Kamfanin Nelplast ya ce kayakin da yake samarwa sun kunshi kaso 60 na robobi, yayin da kasa ya mamaye sauran kaso 40, ba tare da amfani da siminti ba ko kadan, wanda ake ganin ya fi wanda aka saba yi karfi.
Ana sayar da bulo daya na kamfanin kan dala 1 wanda ya fi sauki akan matsakaicin farashin 1.5 da ake sayar da bulo mai siminti. (Fa'iza Msutapha)