in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana ta kaddamar da rahoto game da yaki da yunwa
2018-05-30 09:44:05 cri
A jiya Talata ne, shugaba Nana Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana ya kaddamar da rahoto game da yadda za a yaki yunwa a kasar.

Shirin samar da abinci na duniya shi ne ya bullo da rahoton mai zaman kansa a duk fadin duniya inda zai yi nazari da yin tuntuba kan yadda za a gano manyan kalubalen da za su kai ga nasarar kawar da yunwa a kasashen da ake aiwatar da wannan shiri.

Manufar rahoton, ita ce tabbatar da cimma nasarar manufofin samar da ci gaba mai dorewa kashi na biyu, wadanda za su taimakawa kasar tsara matakan kawo karshen yunwa, da samar da abinci, da ma dukkan nau'o'in karancin abinci mai gina jiki nan da shekarar 2030.

A cewar rahoton, muddin aka samu hadin gwiwa mai karfi tsakanin muhimman sassa dake kawo nakasu ga kokarin samar da abinci da abubuwa masu gina jiki karkashin jagorancin gwamnati, kowane mazaunin kasar ta Ghana, zai samu isasshen abinci mai gina jiki a kowa ce shekara. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China