in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta kaddamar da wani gagarumin shirin samar da aikin yi
2018-05-02 10:24:10 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo, ya kaddamar da wani shirin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin wadanda suka kammala karatu, mai taken "Nation Builders Corps" ko NABCO a takaice.

Cikin shekarar nan kadai, Shirin zai ba da damar samar da aikin yi ga a kalla mutane 100,000 wadanda ke da shaidar digiri, a ma'aikatun gwamnati domin biyan bukatun kasar.

Nana Akufo Addo ya ce rashin aikin yi tsakanin matasa ya kasance abun takaici ga rayuwar al'ummar kasar, kuma a baya-bayan nan, matsalar ta yi kamari biyo bayan haramcin daukar aiki a bangarorin gwamnati da asusun ba da lamuni na duniya ya yi.

Shugaban kasar na da yakinin cewa, zuwa lokacin da za a kammala daukar horo daga shirin na NABCO da zai shafe tsawon shekaru 3, za a magance matsalar rashin gogewa da fasahohin da ake bukata, wadanda ke wa matasan tarnaki wajen samun aikin yi a matsayinsu na sabbin wadanda suka kammala karatu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China