Ya ce yana da muhimmanci a karfafa aikin hukumomi ta yadda za su sanya tsauraran matakan da za su bada damar ganowa tare da hana fitar kudi ba bisa ka'ida ba.
Har ila yau, David Mabuza ya bayyana fitar kudi ba bisa ka'ida ba a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin da kasashe maso tasowa, musamman nahiyar Afrika ke fuskanta a yanzu.
Alkaluman da Tarayyar Afrika ta fitar sun nuna cewa, nahiyar na asarar dala biliyan 80 duk shekara, daga safara kudi ta haramtattun hanyoyi.
A cewar Mabuza, wannan adadin kudi ne da za a iya kashewa kan raya tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa da inganta zaman takewar al'umma da rage gibin da ake samu da kuma basusuuka a fadin nahiyar.
A don haka, ya ce akwai bukatar daukar matakan da suka dace da dokokin da hukunci kan masu aikata laifin don magance matsalar. (Fa'iza Mustapha)