Kwamishinan 'yan sandan jihar, Damian Chukwu, ya ce wasu mutane 7 kuma sun jikkata a harin da aka kai da daren ranar Lahadi.
Damian Chukwu, ya shaidawa manema labarai cewa, maharan sun samu shiga garin ne domin kaddamar da harin ta kauyen Mashimari, dake yankin, ta kusa da wani sansanin 'yan gudun hijira.
Konduga mai yawan jama'ar da suka kai 13,000, ya sha fuskantar hare-haren Boko Haram. Kuma galibin mazauna kauyen sun kasance manoma.
Tun daga shekarar 2009, kungiyar Boko Haram ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 tare da raba wasu miliyan 2.3 da matsugunansu a Nijeriya. (Fa'iza Msutapha)