Wani babban jami'in kungiyar NURTW ya shedawa 'yan jaridu a Abuja, babban birnin kasar cewa, lamarin ya faru ne tsakanin yammacin ranar Talata zuwa safiyar jiya Laraba.
An samu cikakken rahoton faruwar lamarin ne sa'o'i 24 bayan da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da matar wani kwamishina mai ci a jahar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar tare da wasu mutane 6.
Shugaban wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewa, wasu daga cikin direbobin motar da suka tsallake rijiya da baya daga hannun masu garkuwar, sun tabbatarwa 'ya'yan kungiyar yadda lamarin ya faru.
Majiyar ta tabbatar da cewa, mafi yawan fasinjojin da suka hada da mata da kananan yara suna kan hanyarsu ta zuwa Kano ne a lokacin da lamarin ya faru.
Kazamin aikin da masu dauke da makaman suka kaddamar a kwanan nan a kan babbar hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna inda suka yi garkuwa da fasinjoji 107, ya sa babban hafsan sojojin Najeriya, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai, ya baiwa dakarun sojin kasar umarnin su kawo karshe kashe kashe da barnata dokokin jama'a da aka samu a makonni ukun da suka gabata. (Ahmad Fagam)