Birgediya janar Olufemi Akinjobi, shugaban kwamitin karbar alburusai, ya shedawa 'yan jaridu a Abuja, babban birnin kasar cewa, nau'ikan alburusan da kasar ta karba sun hada da roket, bulet da kuma furojektel.
Akinjobi ya kara da cewa, kwamitin ya kuma karbi kayayyakin wasu motocin aiki a filin jirgin Abuja.
A cewarsa, an kawo alburusan ne daga kasashen da sojojin Najeriyar ke yin hadin gwiwa tare da su, sai dai bai bayyana ainihin kasashen da aka kawo alburusan ba.
Haka zalika, babban hafsan sojojin Najeriya laftanal janar Tukur Buratai, ya bada tabbacin cewa, dakarun Najeriyar zasu cigaba da yin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare lafiya da dukiyoyin al'umma da kuma kare ikon yankunan kasar.
Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da yayi da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari don tattauna yanayin da sojojin kasar da kuma yanayin tsaron kasar ke ciki a halin yanzu.
Ya ce tura bataliyar sojojin da aka yi zuwa yankin Birnin Gwari na jahar Kaduna dake arewacin kasar, yayi dai dai da ka'idojin rundunar sojin kasar.(Ahmad Fagam)