Solomon Dalung ya ce akwai wasu mutane da ke yaudarar al'umma ta wannan hanya, suna musu alkawuran karya, don haka ya zama wajibi 'yan kasar su kaucewa fadawa hannu irin wadannan bata gari.
Kalaman ministan na zuwa ne bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci game da shirin da kungiyar Super Eagles ta Najeriya ke yi na tafiya, domin buga gasar cin kofin duniyar cikin nasara.
Ya ce "labarai na zuwa gare mu cewa, ana ta yin wasu abubuwa nan da can, wadanda ke da alaka da yaudarar jama'a, don haka ga masu son zuwa kallo ko goyon bayan tawagar kasar mu ya dace su yi a hankali".
Daga nan sai ministan ya yi kira ga fadar shugaban Najeriyar da ta hanzarta amincewa da kasafin da ake bukata domin cimma nasarar shirye shiryen da kungiyar ta Super Eagles ke yi na halartar gasar ta Rasha. (Saminu Hassan)