in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iska mai karfi ta kashe mutune 6 tare da jikkata mutune 5 a Najeriya
2018-05-19 15:54:49 cri
Kafafen yada labaran cikin gida sun bayyana cewa, wata iska mai karfin gaske a jahar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ta haifar da mummunar barna inda ta hallaka mutane 6, da kuma jikkata wasu mutane 5.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Katsina Aminu Waziri, ya bayyana cewa, kimanin gidaje 500 ne iskar ta lalata da yammacin ranar Alhamis.

Waziri, ya kara da cewa, wani barikin soji da sansanin sojojin sama dake kwaryar birnin Katsinan na daga cikin wuraren da iftila'in ya shafa.

Hukumar mulkin karamar hukumar ta Katsina ya bayyana lamarin da cewa iftila'i ne daga Allah wanda dan adam bai isa ya hana faruwarsa ba, ya ce tuni aka tura jami'ai zuwa yankin domin su duba adadin barnar da iskar ta haddasa, da nufin samar da kayayyakin tallafi ga wadanda bala'in ya shafa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China