Onyema Nwachukwu ya ce cikin wadanda aka kubutar din, akwai mata 33 da yara kanana 16, sai kuma maza guda 4. Hakan dai a cewar jami'in ya biyo bayan wani sumame ne da sojojin suka gudanar a ranar Talata.
Jami'in ya kara da cewa, tuni sojoji suka fara aikin tantance wadanda aka kubutar kafin mika su ga mahukuntan jihar. (Saminu Hassan)




