in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria za ta tasa keyar 'yan ta'adda 105 zuwa Mali
2018-05-29 08:54:00 cri
Algeria za ta tasa keyar 'yan ta'adda 105 'yan asalin Mali zuwa kasarsu.

Jaridar El Watan ta kasar ta ruwaito a jiya Litinin cewa, wata majiya daga hukumomin tsaron kasar ta bayyana cewa, rundunar yaki da ta'addanci ta kasar ce ta kama tsagerun a larduna 5 na kudancin Algeria.

An kama mutanen ne da hannu wajen kafa sansanonin horo a Algeria, domin horar da 'yan kungiyar tsagerun Mali ta Ansar Eddine.

Majiyar ta jaddda cewa, hukumomi na rike da tsagerun, kuma an ayyana su a matsayin mutane masu hadari, wadanda dole a mayar da su kasarsu karkashin matakan tsaro masu tsauri.

Algeria ta yanke shawarar mayar da su ne ta jirgin sama zuwa Bamako, bayan ta tuntubi ofishin Jakadancin Mali dake birnin Algiers.

Gwamnatin Algeria ta girke dubban dakarunta a kan iyakokinta na kudanci da gabashin kasar, a wani yunkuri na dakile kwararar 'yan ta'adda da makamai cikin kasar, a yayin da ake tsaka da fama da rashin kwanciyar hankali a Mali da kuma yakin basasa a Libya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China