Jam'iyyar kwaminis a shirye take ta yi aiki tare da su, domin ba da gudummawarta na hikimomi da kuma karfafa hanyoyin da za su samar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama a duniya baki daya, in ji shugaba Xi, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar da ya aikewa taron karawa juna sani da aka bude a ranar Litinin a birnin Shenzhen dake lardin Guangdong a kudancin kasar Sin.
Taron karawa juna sanin, wanda jam'iyyar CPC ta dauki nauyinsa, ya samu halartar shugabanni da wakilai sama da 100 daga jam'iyyar kwaminis da na kasashen duniya kimanin 50, taron ya sheda cika shekaru 200 ke nan da haihuwar Karl Marx. (Ahmad Fagam)