in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagororin JKS sun jaddada bukatar yin gyaran fuska ga tsarin sanya ido
2018-01-19 20:08:21 cri

Mambobin kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, sun jaddada bukatar da ke akwai ta kafa tsarin sanya ido na duk kasa baki daya, don tabbatar da cewa sha'anin lura da gudanar ayyukan gwamnati sun karade dukkanin sassan kasar baki daya.

Wata sanarwar bayan taro da aka fitar bayan taron jagororin jam'iyyar, ta bayyana sauyin da ake fatan gudanarwa ga tsarin sanya idon, a matsayin manufar siyasa mai matukar ma'ana, wadda za ta shafi dukkanin sassa na kudurori da matakan da za a rika dauka, domin karafafa aikin sanya ido a ayyukan jam'iyyar a cikin gida, da kuma sassan gwamnati baki daya.

An dai fidda sanarwar ce bayan gudanar taro karo na 2 na daukacin mambobin kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a jiya Alhamis a nan birnin Beijing. An kuma amince da kudurin gyaran fuskar yayin taron.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China