Ana saran jami'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin(CPC) za ta yiwa kundin tsarin mulkinta gyaran fuska yayin babban taron mambobin jam'iyyar dake tafe.
A yau ne hukumar kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar ta tattauna game da daftarin yiwa kudin tsarin mulkin jam'iyyar gyaran fuska yayin wani taro da Xi Jinping shugaban kasar Sin kana babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar ya jagoranta a Litinin din nan.
Wata sanarwa da aka fitar bayan taron ta bayyana cewa, gyaran fuskan da ake saran yiwa kundin tsarin mulkin jam'iyyar yayin babban taron mambobin jam'iyyar na 19 bisa la'akari da halin da ake ciki yanzu, zai taimaka wajen yayata ci gaban tsarin gurguzu na musamman mai sigar kasar Sin da kuma yadda za a gina jam'iyyar. A shekarar 2012 ne aka yiwa kundin tsarin mulkin jam'iyyar gyara na karshe. (Ibrahim)