Har ila yau, hukumar ta jaddada aniyarta ta aiwatar da cikakken tsari da daukar tsattsauran matakai kan al'amuran gudanarwar jam'iyyar.
Takardar bayan taron ta aka fitar ta ayyana cewa, a halin yanzu, batun yaki da rashawa aiki ne na ba sani ba sabo, kuma tafiyar da harkokin jami'yyar bisa ka'idojin da aka samar ba abu ne da ba za'a yi sako-sako da shi ba. Dole ne a dauki matakai da basu da karshe wajen yakar ayyukan rashawa, inji takardar bayan taron.