Mambobin hukumar siyasa na kwamitin koli na CPC sun jaddada cewa, kamata ya yi batun martaba shugabancin jam'iyyar da muradun jama'a su kasance ka'idar da za a bi wajen yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.
Shugabannin sun saurari wani rahoto game da shawarwarin da aka tattara daga mambobin jam'iyya da wadanda ba sa cikin jam'iyya game da daftarin shawarar da kwamitin koli na jam'iyyar ya gabatar game da yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska
Daga bisani sun tattauna kan rahoton sannan suka yanke shawarar ci gaba da nazarin daftarin kamar yadda suka tattauna, sa'an nan za su gabatar da daftarin da aka yiwa gyaran fuska ga zama na biyu na kwamitin kolin jam'iyyar na 19 domin ya tantance.
A cewar shawarar da aka cimma yayin zaman, za a gudanar da zama na biyu na kwamitin koli na JKS na 19 daga ranar 18 zuwa 19 ga wannan wata.