Ghassan Salame ya bayyana haka ne jiya a birnin Tripoli, yayin wani taron manema labarai da ya biyo bayan ganawarsa da Mahamed Sayala, Ministan harkokin wajen Gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya.
Ya kara da cewa, ya halarci tarukan tare da Mohamed Sayala, kuma sun tattauna kan yadda za a yi amfani da sakamakon tarukan domin amfanawa cikakken ikon mallakar kasa da 'yancin kan da Libya ke da shi.
A baya-bayan nan ne a ka gudanar da taron kasashen Larabawa a birnin Dhahran na Saudiyya, wanda ya samu halartar shugabannin yankin.
Har ila yau, an gudanar taron kwamitin Ministocin Tarayyar Afrika kwanaki biyu da suka wuce a birnin Addis Ababa na Ethiopia, inda ya bayyana goyon bayansa ga cikakken ikon da tsarin siyasar kasar bisa manufofin MDD, wanda ya dogara da gudanar da zaben kasar kafin karshen bana. (Fa'iza Mustapha)