Kamfanin dillancin labarai na Xinhua, wanda ya samu ganin kwafin rahoton ya bayyana cewa, IAEA na sanya ido ga tsare tsaren kasar Iran, game da ayyukan ta na sarrafa makamashin nukiliya ko JCPOA takaice. Kuma ba wasu alamu na zahiri, dake nuna cewa kasar ta karya yarjejeniyar.
Rahoton ya kara da cewa, Tehran na kiyaye dukkanin ayyuka da suka jibanci sarrafa ruwan sinadarai, da makamashi, da wuraren binciken sarrafa sinadaran nukiliya da dai sauran su, wadanda duka bangarori ne na waccan yarjejeniya.
Wakilan kasashen Sin da Rasha, da Birtaniya, da Faransa, da Jamus da Iran, za su gana a yau Juma'a a birnin Vienna, domin tattauna makomar yarjejeniyar da aka kulla, a zaman da zai kasance na farko tun bayan ficewar Amurka.(Saminu Alhassan)