in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta bukaci EU da ta kara nuna goyon baya ga yarjejeniyar nukiliyar Iran
2018-05-21 10:58:44 cri
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ya bukaci EU da ta kara nuna goyon baya ga yarjejeniyar batun nukiliyar Iran.

Yayin da Zarif yake ganawa da memban kula da harkokin yanayi da makamashi na kungiyar EU Miguel Arias Cañete a jiya Lahadi 20 ga watan nan a birnin Tehran, ya bayyana cewa, kungiyar EU ba ta nuna goyon baya sosai ga yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran ba, don haka mai yiwuwa ne kamfanonin kasashen Turai su ma za su janye daga kasar ta Iran.

Zarif ya yi kira ga kungiyar EU, da ta dauki matakai don kara hadin gwiwa tare da kasar Iran a fannin tattalin arziki. Ya ce, kasar Iran tana fatan kungiyar EU za ta kara zuba mata jari.

A nasa bangare, Cañete ya bayyana cewa, ko da yake kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran, amma kungiyar EU za ta tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar, tare da nuna goyon baya ga kamfanonin kasashen Turai, ta yadda za su ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar ta Iran.

A watan Yuli na shekarar 2015, kasar Iran da kasashe shida wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, suka cimma yarjejeniya kan batun nukiliyar kasar ta Iran. Bisa yarjejeniyar, kasar Iran ta yi alkawarin kayyade shirinta na nukiliya, kana tana da ikon yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, kuma kasashen duniya suka soke takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran. Baya ga hakan, kamfanonin kasashen Turai da dama, sun koma Iran, inda suka daddale yarjejeniyar cinikayya tare da kasar.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a ranar 8 ga wannan wata cewa, kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliyar Iran, za kuma ta sake sakawa kasar takunkumin da aka dage mata bisa cimma waccan yarjejeniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China