Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying wadda ta bayyana hakan Jumma'ar nan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing, ta ce duniya ta kalli yadda shugabannin kasashen biyu suka yi ganawar tarihi a yankin da ya raba kasashen biyu ta kafar talabijin, kuma kasar Sin ta yaba da wannan jarumta da shugabannin suka nuna.
Ta ce shugaba Moon Jae-in ta Koriya ta Kudu da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un, sun tabbatar da buri guda na kawar da makaman nukiliya a yankin. Sun kuma amince su ci gaba da tattaunawa da za ta kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya, bayan ganawarsu ta farko a kan iyakar kauyen Panmunjom a yau Jumma. (Ibrahim Yaya)