in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin Jamus
2018-05-24 20:48:29 cri
Yau Alhamis a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

A yayin ganawar, Xi ya yiwa Merkel maraba da kawo ziyarar Sin karo na 11, ya kuma yabawa Mekel da yadda take mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Xi ya nuna cewa, tun bayan da kasashen biyu suka kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a shekarar 2014, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samu ci gaba sosai, Sin na fatan ci gaba da hada kai tare da Jamus don ciyar da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu gaba.

Baya ga haka, Xi ya nuna cewa, kasar Sin na goyon bayan Turai wajen zaben hanyar neman dunkulewa da kansa, yana ma fatan za a kara tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da budewa juna kofa da kuma samun wadata a tsakanin kasashen EU.

A nata bangaren, Madam Merkel ta bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar mamba ce ta kasashen duniya, ita ma muhimmiyar abokiyar cinikayyar Jamus ce. Kasar Jamus na fatan amfani da sabuwar damar da kasar Sin ke samarwa sakamakon zurfafa bude kofa ga kasashen ketare, don karfafa hadin kan zuba jari a fannin cinikayya da habaka cudanyar al'adu a tsakanin kasashen biyu.

Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan wasu batutuwan dake jawo hankulansu, ciki har da harkokin cinikayyar kasa da kasa da batun nukiliyar Iran da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China