Kwanan baya, Sigmar Gabriel, mataimakin shugabar gwamnatin kasar Jamus ya rubuta wani bayani dake cewa, kasar Sin tana zuba jari da kuma sayen wasu kamfanonin Jamus, a yunkurin samun muhimman fasahohi, amma a sa'i daya, kasashen Turai sun gamu da cikas wajen zuba jari a kasar Sin kai tsaye.
Dangane da bayanin nasa, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Litinin 31 ga wata a nan Beijing cewa, kasar Sin ba ta sauya manufofinta na yin maraba da masu zuba jari daga kasashen ketare ba. Kasar Sin tana son samar da kyakkyawan yanayi mai adalci ga 'yan kasuwa na gida da wajen kasar, ciki har da kasar Jamus, ba ta nunawa kowa bambanci ba, kuma ba ta boye kome ba. (Tasallah Yuan)