in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Kenya za su ziyarci kasar Sin don halartar shirin bada horo na tsaron jiragen kasa
2018-05-24 10:56:23 cri
Kimanin "yan sandan kasar Kenya 30 ne za su ziyarci kasar Sin don halartar shirin bada horo kan tsaron jiragen kasa na tsawon makonni 4 wanda gwamnatin Sin ta dauki nauyi.

Jami'in sashen ciniki da tattalin arziki na ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya Guo Ce, ya jagoranci bikin bankwana da jami'an 'yan sandan a jiya Laraba, ya jaddada cewa, inganta tsaro shi ne babban ginshikin da zai tabbatar da gudanar da ayyukan sufurin jiragen kasan na kasar Kenya (SGR), wanda aka kaddamar da su a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2017.

An zabo 'yan sandan na Kenya ne daga hukumomi masu yawa da suka hada da bangaren sufurin jiragen kasa, da sufuri ta ruwa, da bangaren gandun daji, da masu binciken muggan laifuka domin su halarci shirin bada horon don inganta tsaron lafiyar fasinjoji da kayayyakinsu ta jiragen kasa daga Mombasa zuwa Nairobi.

Shirin bada horon zai kunshi koyarwa a aji, da fita filayen gwaji, da kuma ziyara a wasu cibiyoyi, domin samun kwarewa ga jami'an wajen tsaron lafiyar fasinjojin a jiragen kasan da kayayyaki.

Guo ya ce, ya yi amanna shirin bada horon karkashin dangantakar kasashen biyu zai samar wa jami'an damammaki na kara fahimtar yadda kasar Sin take, za kuma su fahimci yadda yanayin kasar Sin yake, da tarihin ci gaban fannin sufurin jiragen kasa na kasar Sin, da yadda ake dakile ayyukan bata gari a jiragen kasa da dabarun kashe gobara da dai sauransu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China