Jami'ar Nairobi da ofishin MDD mai kula da harkokin zirga-zirgar sararin samaniya(UNOOSA) da hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Japan(JAXA) ne suka kera dan karamin tauraron dan-Adam din mai fadi da tsayi mita goma-goma.
Babban sakatare a ma'aikatar harkokin waje da cinikayyar kasa da kasa ta kasar Kenya Macharia Kamau ya yaba da yadda aka harba tauraron dan-Adan din cikin sararin samaniya, yana mai cewa zai sanya kasar Kenya kasancewa, cibiyar binciken sararin samaniya ta shiyyar.
Kamau ya ce wannan rana ce mai muhimmanci a tarihin binciken sararin samaniya na kasar Kenya, kuma zai taimakawa kasar wajen magance kalubalen da suka shafi matsalar canjin yanayi kamar fari, ambaiyar ruwa da yadda ake hasarar muhallin halittu.
Ya kara da cewa, harba tauraron dan-Adam din zuwa sararin samaniya, zai taimaka a fannin hasashen yanayi da inganta matakan tunkarar bala'u a kasar.(Ibrahim)