in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta karbi bakuncin taron kasashen duniya kan hatimin haraji
2018-05-06 16:27:00 cri

Kasar Kenya za ta karbi bakuncin taron kasa da kasa na yini 3, kan hatimin haraji, wanda zai gudana karon farko a nahiyar Afrika.

Hukumar tattara kudin haraji ta kasar Kenya (KRA), ta ce taron da zai fara daga gobe Litinin a birnin Nairobi, zai tattauna kan tsarin hatimin haraji na yanzu, tare da samarwa da amafani da shirye-shiryen hatimin haraji.

Wata sanarwa da hukumar KRA ta fitar, ta ce taron, zai kuma tattauna kan sabon matakin ingancin hatimin haraji da kuma ci gaban da aka samu na amfani da manhajojin waya wajen tantance ingancin hatimin haraji da kayayyaki.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, taron zai mayar da hankali kan manufofin samar da mafita da za su kare kudaden shigar gwamnati da kuma magance cinikayyar kayayyaki ba bisa ka'ida ba.

Hukumar ta ce taron zai ja hankalin hukumomin gwamnatoci masu sanya haraji da hukumomin hana fasa kauri da jami'an tsaro da masu bincike da masu samar da kayayyaki da masu sayarwa .

A cewar hukumar KRA, aiwatar da shirye-shiryen hatimin haraji na da nufin sa ido kan samar da kayayyakin da shigar da kayyyakin da suka cancanci a sa musu haraji saboda samun kudin shiga.

Manufar taron ita ce, dakile samar da kayayyaki ta haramtacciyar hanya da sayar da su, da rashin bayyana ainihin kayayyakin da ake shigarwa kasa da fasa kauri da kuma samar da jabun kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China