Ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya tare da hadin gwiwar cibiyar Confucius dake jami'ar Nairobi da kungiyar tattalin arziki da cinikayya ta Kenya da Sin(KCETA) ne suka shirya gasar, wadda ta hallara matasa 16 wadanda suka nuna kwarewarsu ta magana da harshen Sinanci.
A jawabinsa jami'in ofishin jakadancin Sin dake Kenya Li Xuhang, ya yabawa matasan da suka shiga wannan gasa, yana mai cewa harshe muhimman bangare ne wajen bunkasa musayar al'adu.
Li ya yi imanin cewa, ta hanyar wannan gasa, matasan za su kara fahimtar harshe da al'adun Sinawa.
Ya kuma bayyana cewa, yadda ake koyar da Sinanci da al'adun Sinawa ya bunkasa kwarai a kasar Kenya. Ya kuma mika godiya ga yadda aka bude cibiyoyin Confucius har guda hudu a manyan jami'o'in kasar.
An gabatar da jawabai da kade-kade da raye-raye da tsoffin wake-wake da sauran fasahohi yayin gasar da aka gudanar a tsohuwar jami'ar Kenya.(Ibrahim)