in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 132 sun rasu sakamakon bala'in ambaliyar ruwa a Kenya
2018-05-10 10:43:23 cri

Bisa labarin da aka samu a jiya Laraba, an ce, mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar Kenya ya fidda sanarwar cewa, bayan shiga watan Maris na bana, ya zuwa yanzu, ana ta fama da bala'un ambaliyar ruwa a kasar Kenya sakamakon ruwan sama mai karfi da ake yi a kasar, lamarin ya riga ya haddasa rasuwar mutane 132, yayin da mutane sama da dubu 220 suka rasa gidajensu.

Yanayin damina na bana ya tsawaita a kasar Kenya, kuma ana ruwan sama mai karfi a wurare da dama a kasar, wanda hakan ke gurgunta zirga-zirga cikin wasu unguwannin dake babban birnin kasar, wato Nairobi da kuma a birnin Mombasa.

Babban sakataren kungiyar Red Cross ta kasar Kenya ya bayyana cewa, a kalla kananan hukumomi guda 32, dake cikin kananan hukumomin kasar Kenya guda 47 suna fama da matsalolin ambaliyar ruwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China