A cikin sanarwar da kungiyar ta bayar, an ce yankunan da suka fi fama da bala'in sun hada da Nairobi, babban birnin kasar, da Kisumu da Nourke dake yammacin kasar, da Kirifi da Tana dake gabashin kasar, da Marcueni da wasu gundumomin dake kudancin kasar, da kuma wasu gundumomin dake arewacin kasar.
Sanarwar ta ce, bala'in ambariyar ruwa ya lalata gidajen fararen hula da gandun noma da dama, kana an rushe wasu manyan kayayyakin more rayuwa, ciki har da hanyoyin mota, baya ga rasuwar dabbobin gida da yawa da hakan ya haifar.
Baya ga haka, sanarwar ta ce, kungiyar ba da agaji ta red cross ta kasar, ta riga ta aika da ma'aikata zuwa yankunan dake fama da bala'in, don gudanar da ayyukan ceto, da kuma samar da hidimar kiwon lafiya. (Bilkisu)