in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Rwanda da Habasha za su ziyarci rukunin masana'antun da kasar Sin ta gina
2018-05-24 10:37:37 cri
Gwamnatin kasar Habasha ta sanar a jiya Laraba cewa, firaiministan kasar Abiy Ahmed da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame za su ziyarci rukunin masana'antu na Hawassa dake Habashan a gobe Juma'a.

Wata sanarwar da jami'in ofishin yada labarai na gwamnatin Habashan (GCAO) ya fitar ya bayyana cewa, a ziyarar aikin kwanaki uku da shugaba Kagame ya kai kasar Habashan, an tsara ziyarar da zai kai rukunin masana'antun wanda kasar Sin ta gina.

Rukunin masana'antu na Hawassa, wanda gwamnatin kasar Habasha ta dauke shi a matsayin wani abin koyi daga cikin rukunonin masana'antu da ake ginawa a duk fadin kasar, ya samu gagarumar nasara tun bayan da aka kaddamar da shi a watan Yulin shekarar 2016, musamman bisa yadda suka janyo hankalin manyan kamfanonin saka tufafi na duniya, kana sun janyo hankalin kamfanonin zuwa kasar.

Sanarwar GCAO ta ce, ziyarar da Kagame zai kai zuwa rukunin masana'antun Hawassa da sauran kayayyakin more rayuwa dake Habashan, ana sa ran zai kasance kyakkyawan abin koyi wanda Rwandan za ta koya daga kasar.

A kwanakin baya, gwamnatin Habasha ta sanar da shirinta inda take sa ran samun kudaden shiga na dalar Amurka biliyan guda a duk shekara daga rukunin masana'antun da zarar ya fara aiki. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China