in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha tana adawa da kudurin da Amurka ta zartas dangane da ita
2018-04-12 10:57:52 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha ta ba da wata sanarwa a ranar 11 ga wata cewa, majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da wani kuduri na zargi game da yanayin jin kai da halin gudanar da ayyukan kasa da gwamnatin Habasha take yi, inda a ganinta wannan kuduri ya musanta gaskiya kuma bai dace da halin da ake ciki a kasar ba.

An ce, a ranar 10 ga wata, majalisar wakilan Amurka ta zartas da wani kudurin yin kira ga Habasha da ta kawar da halin dokar ta baci da ta tsayar a kwanakin baya, da kuma kawo karshen yin amfani da karfin tuwo da bincike kan matsalar kisan kai da aka yi.

A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Habasha ta bayar a wannan rana, an ce, kudurin da Amurka ta bayar ba shi da amfani ga bunkasuwar dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu, har ma zai kawo illa ga mulkin kan kasar Habasha. Sanarwar ta ce, gwamnatin Habasha tana yin iyakar kokarinta na kiyaye mulkin jama'arta da kyautata gwamnatinta. Hakazalika, sanarwar ta jaddada alkawarin da gwamnatin Habasha take yi na sa kaimi ga samun adalci, 'yanci da gudanar da ayyukan kasa bisa doka. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China