in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Makon cinikayya ta kasar Sin ya hada Sinawa masu sayar da kayayyaki da 'yan kasar Habasha masu saye, karkashin inuwa guda
2018-05-06 16:50:11 cri

Makon cinikayya na kasar Sin karo na 2, wanda ya gudana a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, ya kawo karshe a jiya Asabar, inda kamfanonin kasar Sin kusan 50 suka baje hajojinsu domin jan hankalin al'ummar Habasha masu saye.

Makon ya gudana ne karon farko a Addis Abban Habasha, daga ranar 4 zuwa 6, na watan Yulin 2017.

Makon cinikayya na kasar Sin a Habasha, na samun goyon bayan cibiyar cinikayya ta kasar Sin da kuma majalisar dake karfafa cinikayya tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin.

Shirin da ya shafe kwanaki 3, ya samu halartar kamfanonin kasar Sin daban-daban na fannonin samar da kayayyakin gine-gine da injuna da kayayyakin laturoni da na abinci da sha da robobi da abubuwan bukata na yau da kullum da na kiwon lafiyar dabbobi da sauransu.

Kididdiga ta nuna cewa, a yanzu, kasar Sin ita ce babbar abokiyar cinikayyar Habasha, inda cikin watanni 6 na farkon shekarar kudi ta 2017/2018 ta Habasha, kasar ta fitar da kayayyakin da darajarsu ta kai dala biliyan 144.5 zuwa kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China