in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WFP ya yabawa shirin Sin na samar da agajin jin kai ga Habasha
2018-05-16 09:59:26 cri
Shirin samar da abinci na MDD (WFP) ya yabawa kasar Sin game da samar da agajin jin kai ga 'yan gudun hijira da kuma mutanen da fari ya shafa a kasar Habasha.

Paul Anthem, shugaban sashen sadarwa da hulda da jama'a na shirin WFP a Habasha, ya bayyana a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, shirin samar da abinci na MDDr ya karbi tallafin kayayyaki masu yawa daga gwamnatin Sin a cikin shekaru masu yawa, musamman samar ta tallafin abinci mai gina jiki.

Anthem ya ce, yawanci suna samun tallafin daga kasar Sin ne a daidai lokacin da kasar Habashan ke cikin matsanancin halin bukatar tallafin jin kai, kana yayin da miliyoyin 'yan kasar ke bukatar taimakon abinci mai gina jiki.

Ya ce taimakon yana tafiya ne kai tsaye ga mutane masu karamin karfi wadanda ke cikin halin karancin abinci mai gina jiki.

A bisa wata kididdiga da hukumar kiyaye aukuwar bala'o'i ta kasar Habasha ta fitar ya nuna cewa, a zagaye hudu na tallafin, ta hanyar mu'amala tsakanin kasashen biyu da mu'amalar gamayyar kasa da kasa, kawo yanzu, kasar Sin ta samar da taimakon jin kai ga Habasha wanda aka kiyasa adadin kudin da ya kai dalar Amurka miliyan 36.6, hakan ya sa kasar Sin ta zama kasa ta uku mafi samar da taimakon abinci mai yawa ga kasar Habasha. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China